Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Friendship

31 ayoyi · 1 fanni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Man shafawa mai ƙanshi da kuma turare kan faranta zuciya, gaisuwar amini kuma takan fito daga shawarar kirki.

  2. Kada ka manta da abokinka da kuma abokin mahaifinka, kuma kada ka tafi gidan ɗan’uwanka sa’ad da masifa ta same ka, gara ka je wurin maƙwabci na kusa da ka je wurin ɗan’uwan da yake da nisa.

  3. Biyu sun fi ɗaya, gama suna samun riba mai kyau na aikinsu.

  4. In ɗaya ya fāɗi, abokinsa zai taimake shi yă tashi. Amma abin tausayi ne ga mutumin da ya fāɗi ba shi kuma da wanda zai taimake shi yă tashi!

  5. In mutum biyu sun kwanta tare, za su ji ɗumin juna. Amma yaya mutum ɗaya zai ji ɗumi yana shi kaɗai?

  6. Ana iya shan ƙarfin mutum ɗaya, mutum biyu za su iya kāre kansu. Igiya riɓi uku tana da wuya tsinkawa.