- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Creeping Things
Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki
“ ‘Dukan ƙwarin da suke da fikafikai masu tafiya da ƙafafu huɗu abin ƙyama ne gare ku.
Sai dai akwai ƙwarin da suke da fikafikai masu tafiya da ƙafafu huɗu da za ku ci; waɗanda suke da cinyoyin da suke sa su iya tsalle.
Za ku iya cin kowane irin fāra, gyare, ƙwanso da danginsu.
Amma sauran ƙananan ƙwari duka masu fikafikai, suna kuma jan ciki, abin ƙyama ne a gare ku.
“ ‘Waɗannan ƙananan dabbobi da suke rarrafe a ƙasa, haram ne a gare ku, wato, murɗiya, da ɓera, da gafiya da irinsa,
da tsaka, da hawainiya, da ƙadangare, da guza, da damo.
Dukan waɗanda suke rarrafe, za su zama marasa tsarki gare ku. Duk wanda ya taɓa su sa’ad da suka mutu, zai zama ƙazantacce har zuwa yamma.
Duk abin da mushensu ya fāɗa a kai, zai ƙazantu. Ko a kan itace ne, ko a bisa tufafi, ko a fata, ko a buhu, ko cikin kowane irin abu da ake amfani da shi, to, tilas a sa shi cikin ruwa, zai zama ƙazantacce har zuwa yamma, sa’an nan zai tsarkaka.
In waninsu ya fāɗi a cikin tukunyar laka, kome da yake a tukunyar zai ƙazantu, kuma dole a fashe tukunyar.
Duk abincin da aka yarda a ci, wanda ya taɓa ruwa daga irin tukunyan nan zai zama marar tsabta, kuma duk ruwan da za a sha daga irin tukunyan nan ƙazantacce ne.
Kowane irin abu da mushensu ya fāɗa a kai ya ƙazantu ke nan; ko a kan murhu, ko a tukunyar dahuwa, dole a farfashe su. Su haramtattu ne kuma dole ku ɗauke su haramtattu.
Maɓuɓɓuga ko tafki na tarin ruwa zai ci gaba da zauna mai tsabta, amma duk wanda ya taɓa ɗaya daga cikin waɗannan gawawwakin ya haramtu.
In gawa ta fāɗi a irin da za a shuka, irin zai ci gaba da zama mai tsabta.
Amma in an sa ruwa a irin sai kuma gawar ta fāɗi a kai, to, irin ya zama haram gare ku.
“ ‘In dabbar aka yarda a ci ta mutu, duk wanda ya taɓa gawarta zai ƙazantu har yamma.
Duk wanda ya ci wani sashe na gawar dole yă wanke rigunansa, kuma zai ƙazantu har yamma. Duk wanda ya ɗauki gawar dole yă wanke rigunansa, zai kuwa ƙazantu har yamma.
“ ‘Duk dabba mai rarrafe a ƙasa abin ƙyama ne; ba kuwa za a ci shi ba.
Ba za ku ci wani halittar da take rarrafe a ƙasa, ko tana jan ciki, ko tana tafiya a kan ƙafafu huɗu, ko a kan ƙafafu da yawa ba; abin ƙyama ne.
Kada ku ƙazantar da kanku ta wurin wani daga waɗannan halittu. Kada ku ƙazantar da kanku ta dalilinsu, ko a mai da ku haramtattu ta wurinsu.
Ni ne Ubangiji Allahnku; ku tsarkake kanku ku kuma zama da tsarki, domin Ni mai tsarki ne. Kada ku ƙazantar da kanku ta wurin wani halittar da take rarrafe a ƙasa.