Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Creeping Things: A general term for animals

7 ayoyi · 4 fannoni

Ayoyi game da A general term for animals

  1. “ ‘Dukan ƙwarin da suke da fikafikai masu tafiya da ƙafafu huɗu abin ƙyama ne gare ku.

  2. Sai dai akwai ƙwarin da suke da fikafikai masu tafiya da ƙafafu huɗu da za ku ci; waɗanda suke da cinyoyin da suke sa su iya tsalle.

  3. Za ku iya cin kowane irin fāra, gyare, ƙwanso da danginsu.

  4. Amma sauran ƙananan ƙwari duka masu fikafikai, suna kuma jan ciki, abin ƙyama ne a gare ku.

  5. “ ‘Waɗannan ƙananan dabbobi da suke rarrafe a ƙasa, haram ne a gare ku, wato, murɗiya, da ɓera, da gafiya da irinsa,

  6. da tsaka, da hawainiya, da ƙadangare, da guza, da damo.

  7. Dukan waɗanda suke rarrafe, za su zama marasa tsarki gare ku. Duk wanda ya taɓa su sa’ad da suka mutu, zai zama ƙazantacce har zuwa yamma.