Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Christian Conduct: Blessedness of maintaining

16 ayoyi · 48 fannoni

Ayoyi game da Blessedness of maintaining

  1. Mai farin ciki ne mutumin da ba ya aiki da shawarar mugaye ko yă yi abin da masu zunubi suke yi ko yă zauna tare da masu yin ba’a.

  2. Amma yana jin daɗin bin dokar Ubangiji, kuma yana ta nazarinta dare da rana.

  3. Yana kama da itacen da aka shuka kusa da maɓulɓulan ruwa, wanda yake ba da amfani a daidai lokaci wanda kuma ganyensa ba sa bushewa. Duk abin da yake yi, yakan yi nasara.

  4. Tsoron Ubangiji yakan kawo tsabtar zuciya, zai kasance har abada. Farillan Ubangiji tabbatattu ne, kuma gaba ɗaya masu adalci ne.

  5. Sun fi zinariya daraja, fiye da zalla zinariya nesa; sun fi zuma zaƙi fiye da zuma daga kaki.

  6. Ta wurinsu ana gargaɗe bawanka; a kiyaye su akwai lada mai girma.

  7. “Masu albarka ne waɗanda suke matalauta a ruhu, gama mulkin sama nasu ne.

  8. Masu albarka ne waɗanda suke makoki, gama za a yi musu ta’aziyya.

  9. Masu albarka ne waɗanda suke masu tawali’u, gama za su gāji duniya.

  10. Masu albarka ne waɗanda suke jin yunwa da ƙishirwa don gani an yi adalci, gama za a ƙosar da su.

  11. Masu albarka ne waɗanda suke masu jinƙai, gama za a nuna musu jinƙai.

  12. Masu albarka ne waɗanda suke masu tsabtar zuciya, gama za su ga Allah.

  13. Masu albarka ne waɗanda suke masu ƙulla zumunci, gama za a kira su ’ya’yan Allah.

  14. Masu albarka ne waɗanda ake tsananta musu don gani an yi adalci, gama mulkin sama nasu ne.

  15. “Masu albarka ne ku, sa’ad da mutane suke zaginku, suna tsananta muku, suna kuma faɗin kowace irin muguwar magana a kanku saboda ni.

  16. Ku yi murna ku kuma yi farin ciki, domin ladarku mai yawa ne a sama, gama haka suka tsananta wa annabawan da suka riga ku.