Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Carving

11 ayoyi · 3 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. Duk masu yin gumaka ba kome ba ne, da kuma abubuwan da suke ɗauka da daraja banza ne. Waɗanda za su yi magana a madadinsu makafi ne; jahilai ne, marasa kunya.

  2. Waɗanda suke siffanta allah su kuma yi zubin gunki, waɗanda ba za su yi musu ribar kome ba?

  3. Shi da irinsa za su sha kunya; masu sassaƙa ba kome ba mutane ne kurum. Bari su tattaru su ɗauki matsayinsu; za su firgita su kuma sha mummunan kunya.

  4. Maƙeri yakan ɗauki kayan aiki ya yi aiki da shi a cikin garwashi; ya ƙera gunki da guduma, ya gyara shi da hannuwansa masu ƙarfi. Yakan ji yunwa ya kuma rasa ƙarfi; yakan sha ruwa ya kuma ji gajiya.

  5. Kafinta yakan gwada katako yă kuma zāna siffar da alli; yă goge shi da kayan aiki yă kuma zāna shi da alƙalami. Yă siffanta shi a kamannin mutum, mutum cikin dukan darajarsa, don yă ajiye shi a cikin masujada.

  6. Yakan ka da itacen saifires, ko kuwa ya ɗauki saifires ko oak. Yă bar shi yă yi girma a cikin itatuwan kurmi, ko yă shuka itacen fir, ruwan sama kuma yă sa yă yi girma.

  7. Abin hura wutar mutum ne; yakan ɗebi waɗansu yă hura wuta don yă ji ɗumi, ya hura wuta yă gasa burodi. Amma yakan ƙera zinariya yă kuma yi masa sujada; yakan yi gunki sa’an nan yă rusuna masa.

  8. Rabin katakon yakan ƙone a wuta; a kansa yakan dafa abincinsa, yă gasa namansa yă kuma ci sai ya ƙoshi. Yakan ji ɗumi yă kuma ce, “Aha! Na ji ɗumi; na gan wutar.”

  9. Da sauran itacen yakan yi allah, gunkinsa; yă rusuna masa yă kuma yi sujada. Yakan yi masa addu’a yă ce, “Ka cece ni; kai ne allahna.”

  10. “Ina amfanin gunki da mutum ne ya sassaƙa? Ko siffar da take koyar da ƙarya? Gama wanda ya yi shi yana dogara ne ga halittarsa; ya yi gumakan da ba sa magana.

  11. Kaito wanda ya ce da katako, ‘Rayu!’ Ko kuwa dutse marar rai, ‘Farka!’ Zai iya bishewa ne? An dalaye shi da zinariya da azurfa; ba numfashi a cikinsa.”