Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Beds: Reclining on at meals

9 ayoyi · 28 fannoni

Ayoyi game da Reclining on at meals

  1. Sai ya ƙi. Ya ce, “Ba zan ci abinci ba.” Sai da bayinsa da matar suka roƙe shi, sa’an nan ya ji maganarsu, ya tashi daga ƙasa, ya zauna a bakin gado.

  2. Matar kuwa tana da maraƙin da take kiwo a gida, sai ta ɗauke shi nan da nan ta yanka. Ta ɗauki garin fulawa ta kwaɓa, ta yi waina marar yisti.

  3. Sai ta kawo wa Shawulu da bayinsa suka kuwa ci. A daren nan suka tashi suka tafi.

  4. Kuna kwanciya a kan gadajen da aka yi musu shimfiɗar hauren giwa kuna mimmiƙe a kan kujerunku. Kuna cin naman ƙibabbun raguna da na ƙosassun ’yan maruƙa.

  5. Kuna kaɗa molayenku yadda Dawuda ya yi kuna ƙirƙiro waƙoƙi a kan kayan kaɗe-kaɗe.

  6. Da manyan kwanoni kuke shan ruwan inabi kuna kuma shafa mai mafi kyau, amma ba kwa baƙin ciki game da kangon da Yusuf ya zama.

  7. To, ana nan, sai ɗaya daga cikin Farisiyawa ya gayyaci Yesu cin abincin yamma a gidansa, ya kuwa tafi gidan Bafarisiyen, ya zauna a tebur.

  8. Da wata mace wadda ta yi rayuwar zunubi a wannan gari ta ji Yesu yana cin abinci a gidan Bafarisiyen, sai ta kawo ɗan tulun turaren alabasta,

  9. ta kuma tsaya daga bayansa, wajen ƙafafunsa tana kuka, sai hawayenta sun fara zuba a ƙafafunsa. Sai ta goge su da gashin kanta, ta sumbace su, sa’an nan ta shafa musu turare.