Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Balaam

29 ayoyi · 8 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Sun bar miƙaƙƙiyar hanya suka bauɗe suna bin hanyar Bala’am ɗan Beyor, wanda ya yi ƙaunar hakkin mugunta.

  2. Amma an tsawata masa saboda laifinsa ta wurin jaki, dabbar da ba ta magana, wadda ta yi magana da muryar mutum ta kuma kwaɓi haukan annabin.

  3. Duk da haka, ina da abubuwa kima game da kai. Kana da mutane a can waɗanda suke riƙe da koyarwar Bala’am, wanda ya koya wa Balak yă ja hankalin Isra’ilawa su yi zunubi ta wurin cin abincin da aka miƙa wa gumaka hadaya, su kuma yi fasikanci.

  4. Haka ma kana da waɗanda suke riƙe da koyarwar Nikolaitawa.