Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Absalom: Children of
Ayoyi game da Children of
Aka haifa wa Absalom ’ya’ya uku maza da ’ya mace guda. Sunanta Tamar, ta kuwa zama kyakkyawan mace ƙwarai.
A lokacin da Absalom yake da rai, Absalom ya gina wa kansa al’amudin tunawa, a Kwarin Sarki, gama ya yi tunani ya ce, “Ba ni da ɗa namiji wanda zai sa a riƙa tunawa da ni.” Sai ya kira ginshiƙin da sunansa, ana kuwa kira shi Al’amudin Absalom har wa yau.
ya kuma yi mulki a Urushalima shekara uku. Sunan mahaifiyarsa Ma’aka ne, ’yar Abisalom.
Sa’an nan ya auri Ma’aka ’yar Absalom, wadda ta haifa masa Abiya, Attai, Ziza da kuma Shelomit.