Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Abomination

20 ayoyi · 1 fanni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. Kada mace ta sa suturar maza, kada kuma namiji ya sa suturar mata, gama Ubangiji Allahnku yana ƙyamar duk mai yin haka.

  2. Gama Ubangiji yana ƙyama mai aikata mugunta amma yakan rungumi adalin da ya amince da shi.

  3. Akwai abubuwa shida da Ubangiji ya ƙi, abubuwa bakwai da suke abin ƙyama gare shi,

  4. duban reni, harshe mai ƙarya, hannuwa masu zub da jinin marar laifi,

  5. zuciyar da take ƙulla mugayen dabaru, ƙafafun da suke sauri zuwa aikata mugunta,

  6. mai shaidar ƙarya wanda yake zuba ƙarairayi, da kuma mutumin da yake tā-da-na-zaune-tsaye a cikin ’yan’uwa.

  7. Bakina yana magana abin da yake gaskiya, gama leɓunana sun ƙi mugunta.

  8. Ubangiji yana ƙyamar mutane masu muguwar zuciya amma yana jin daɗin waɗanda hanyoyinsu ba su da laifi.

  9. Ubangiji yana ƙyamar leɓunan masu ƙarya, amma yana jin daɗin mutanen da suke masu gaskiya.

  10. Ubangiji yana ƙyamar hadayar mugaye, amma addu’ar masu aikata gaskiya kan sa ya ji daɗi.

  11. Ubangiji yana ƙin hanyar mugaye amma yana ƙaunar waɗanda suke neman adalci.

  12. Ubangiji yana ƙyamar tunanin mugaye, amma waɗanda suke da tunani masu tsabta yakan ji daɗinsu.

  13. Ubangiji yana ƙyamar dukan zuciya mai girman kai. Ka tabbata da wannan. Ba za su kuɓuta daga hukunci ba.

  14. Baratar da mai laifi a kuma hukunta mai adalci, Ubangiji ya ƙi su biyu.

  15. Ma’auni marar gaskiya da magwajin da ba daidai ba, Ubangiji ya ƙi su duka.

  16. Ubangiji ya ƙi ma’aunin da ba daidai ba, da kuma magwajin da ba su gamshe shi ba.

  17. Hadayar mugaye abin ƙyama ne, balle ma in aka kawo da mugun nufi!

  18. Makircin wawa zunubi ne, mutane kuma sukan yi ƙyamar mai ba’a.

  19. In wani ya yi kunnuwa ƙashi ga doka ko addu’arsa ma abar ƙyama ce.

  20. Masu adalci suna ƙyamar masu rashin gaskiya; mugaye sukan yi ƙyamar masu aikata gaskiya.