Tsallake zuwa abun ciki

Elisha

53 ayoyi · 1 ɗan gida

An kuma san shi da: Eliseus

Ayoyin da suka ambaci Elisha

Tace bisa littafi
  1. Elisha ya mutu, aka kuma binne shi. To, mahara Mowabawa sun saba kawo hari a ƙasar Isra’ila a kowace bazara.

  2. Wata rana yayinda waɗansu Isra’ilawa suke binne wani mutum, farat ɗaya sai ga mahara; saboda haka suka jefar da gawar mutumin a kabarin Elisha. Da gawar ta taɓa ƙasusuwan Elisha, sai mutumin ya farka, ya tashi ya tsaya da ƙafafunsa.

  3. Akwai kuma mutane da yawa a Isra’ila masu kuturta a zamanin annabi Elisha, amma ba ko ɗayansu da aka tsarkake sai Na’aman mutumin Suriyan nan kaɗai.”