Tsallake zuwa abun ciki

Daughter of Lot - Younger

7 ayoyi · 5 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci Daughter of Lot - Younger

  1. Duba, ina da ’ya’ya mata biyu waɗanda ba su taɓa sanin namiji ba, bari in kawo muku su ku yi kome da kuke so da su. Amma kada ku taɓa waɗannan mutane, gama su baƙina ne kuma dole in tsare su.”

  2. Mutanen nan biyun suka ce wa Lot, “Kana da wani a nan, ko surukai, ko ’ya’ya maza ko mata, ko kuwa wani dai a cikin birni wanda yake naka? Ka fitar da su daga nan,

  3. Saboda haka Lot ya tafi ya yi magana da surukansa waɗanda suka yi alkawari za su aure ’ya’yansa mata. Ya ce, “Ku yi sauri ku fita daga wannan wuri, gama Ubangiji yana gab da hallaka birnin.” Amma surukansa suka ɗauka wasa yake yi.

  4. Gari na wayewa, sai mala’ikun nan suka ƙarfafa Lot suna cewa, “Yi sauri! Ka ɗauki matarka da ’ya’yanka biyu mata waɗanda suke a nan, don kada a shafe ku sa’ad da ake hukunta birnin.”

  5. Da yana jan jiki, sai mutanen suka kama hannunsa da hannuwan matarsa da na ’ya’yansa biyu mata, suka kai su bayan birni, gama Ubangiji ya nuna musu jinƙai.

  6. Lot da ’ya’yansa biyu mata suka bar Zowar suka kuma zauna a cikin duwatsu, gama ya ji tsoro yă zauna a Zowar. Shi da ’ya’yansa biyu mata suka zauna a ciki wani kogo.

  7. Ta haka ’ya’yan Lot biyu mata duk suka yi ciki daga mahaifinsu.