Tsallake zuwa abun ciki

Ayuba25

Jawabin Bildad na ƙarshe, gajere

1
Sai Bildad mutumin Shuwa ya amsa,

Mulkin Allah cikakke

2
“Mulki na Allah ne, dole a ji tsoronsa; yana tafiyar da kome yadda ya kamata a cikin sama.
3
Za a iya ƙirga rundunarsa? A kan wane ne ba ya haska haskensa?

Rashin tsarkin ’yan Adam

4
Ta yaya mutum zai iya zama mai adalci a gaban Allah? Ta yaya mutumin da mace ta haifa zai zama mai tsarki?
5
In har wata da taurari ba su da tsarki a idanunsa,
6
mutum fa? Ai, wannan tsutsa ne, ɗan ƙwaro kawai. Me mutum ya daɗa a gaban Allah!”
Use arrow keys to navigate
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Reading Width 45 chars

Options