Ru’uya ta Yohanna 1:13-16
13
A tsakiyar alkukan kuwa akwai wani “kama da ɗan mutum,” saye da rigar da ya kai har ƙafafunsa da kuma ɗamarar zinariya daure a ƙirjinsa.
14
Kansa da kuma gashin fari ne fat kamar ulu, fari kamar dusar ƙanƙara, idanunsa kuwa kamar harshen wuta.
15
Sawunsa sun yi kamar tagullar da take haske cikin matoya, muryarsa kuma ta yi kamar muryar ruwaye masu gudu.
16
A hannunsa na dama ya riƙe taurari bakwai, daga bakinsa kuwa takobi mai kaifi biyu ya fito. Fuskarsa ta yi kamar rana mai haskakawa da dukan haskenta.
Settings