Ru’uya ta Yohanna 2:1-7
1
“Zuwa ga mala’ikan ikkilisiya a Afisa, ka rubuta, Waɗannan su ne kalmomi na wannan wanda yake riƙe da taurari bakwai a hannunsa na dama yana kuma tafiya a tsakanin alkukan fitilu bakwai na zinariya.
2
Na san ayyukanka, faman aikinka da daurewarka. Na san cewa ba ka iya haƙuri da mugayen mutane, ka gwada waɗanda suke cewa su manzanni ne, alhali kuwa ba haka ba ne, ka kuwa tarar cewa su na ƙarya ne.
3
Kai kam ka daure ka kuma jimre da wahala saboda sunana, ba ka kuwa gaji ba.
4
Duk da haka ina riƙe da wannan game da kai. Ka watsar da ƙaunarka ta farko.
5
Ka tuna da matsayinka a dā kafin ka fāɗi! Ka tuba ka kuma yi ayyukan da ka yi da fari. In ba ka tuba ba, zan zo wajenka in ɗauke wurin ajiye fitilanka daga inda yake.
6
Sai dai kana da wannan abu mai kyau. Ka ƙi ayyukan Nikolaitawa da ni ma nake ƙi.
7
Duk mai kunnen ji, yă ji abin da Ruhu yake faɗa wa ikkilisiyoyi. Duk wanda ya ci nasara, zan ba shi ikon ci daga itacen rai, da yake cikin aljannar Allah.
Settings