Zabura 78:43-51
43
ranar da ya nuna mu’ujizansa a Masar abubuwan banmamakinsa a yankin Zowan ba.
44
Ya mai da kogunansu suka zama jini; ba su iya sha daga rafuffuka ba.
45
Ya aika da tarin ƙudajen da suka cinye su, da kwaɗin da suka wahalshe su.
46
Ya ba da hatsinsu ga fāra, amfanin gonakinsu ga ɗango.
47
Ya lalace inabinsu da ƙanƙara itatuwan al’ul nasu kuma da jaura.
48
Ya miƙa shanunsu ga ƙanƙara, tumakinsu ga aradun tsawa.
49
Ya saki musu fushinsa mai zafi, hasalarsa, zafin rai da kuma ɓacin ransa, ƙungiyar mala’iku masu hallakarwa.
50
Ya shirya hanya wa fushinsa; bai tsare ransu daga mutuwa ba amma ya miƙa su ga annoba.
51
Ya bugi kowane ɗan fari na Masar, mafari ƙarfin mazantakansu a tentunan Ham.
Settings