Zabura 78:34-39
34
A duk sa’ad da Allah ya kashe su, sai su neme shi; sukan juyo a natse gare shi.
35
Sun tuna cewa Allah ne Dutsensu, cewa Allah Mafi Ɗaukaka ne Mai fansarsu.
36
Amma sai su yi ta yin masa zaƙin baki, suna masa ƙarya da harsunansu;
37
zukatansu ba sa biyayya gare shi, ba su da aminci ga alkawarinsa.
38
Duk da haka ya kasance mai jinƙai; ya gafarta laifofinsu bai kuwa hallaka su ba. Sau da sau ya janye fushinsa bai kuwa sa fushinsa yă ƙuna ba.
39
Ya tuna cewa su naman jiki ne kawai, iska mai wucewa da ba ta dawowa.
Settings