Zabura 78:17-33
17
Amma suka ci gaba da yin masa zunubi, suna tayarwa a cikin hamada a kan Mafi Ɗaukaka.
18
Da gangan suka gwada Allah ta wurin neman abincin da suke kwaɗayi.
19
Suka yi magana a kan Allah, suna cewa, “Allah zai iya shimfiɗa tebur a cikin hamada?
20
Sa’ad da ya bugi dutse, ruwa ya ɓulɓulo, rafuffuka suka yi gudu a yalwace. Amma zai iya ba mu abinci? Zai iya tanada wa mutanensa nama?”
21
Sa’ad da Ubangiji ya ji su, ya yi fushi ƙwarai; wutarsa ta ɓarke a kan Yaƙub, hasalarsa kuwa ta tashi a kan Isra’ila,
22
gama ba su gaskata ga Allah ba ko su dogara ga cetonsa.
23
Duk da haka ya ba da umarni ga sarari a bisa ya kuma buɗe ƙofofin sammai;
24
ya sauko da Manna wa mutanensa don su ci, ya ba su hatsin sama.
25
Mutane suka ci burodin mala’iku; ya aika musu dukan abincin da za su iya ci.
26
Ya saki iskar gabas daga sammai ya kuma saki iskar yamma ta wurin ikonsa.
27
Ya sauko da nama a kansu kamar ƙura, tsuntsaye masu firiya kamar yashi a bakin teku.
28
Ya sa suka sauka a cikin sansaninsu, ko’ina kewaye da tentunansu.
29
Suka ci har suka sami fiye da abin da ya ishe su, gama ya ba su abin da suka yi kwaɗayi.
30
Amma kafin su juyo daga abincin da suka yi kwaɗayi, kai tun ma yana a bakunansu,
31
fushin Allah ya ƙuna a kansu; ya karkashe waɗanda suka fi ƙiba a cikinsu, yana yankan matasan Isra’ila.
32
Duk da haka, suka ci gaba da yin zunubi; duk da abubuwan banmamakinsa, ba su gaskata ba.
33
Saboda haka ya sa kwanakinsu suka ƙare a banza shekarunsu kuma cikin masifa.
Settings