Ƙidaya 13:1-20
1
Ubangiji ya ce wa Musa,
2
“Ka aiki waɗansu mutane zuwa ƙasar Kan’ana, wadda nake ba Isra’ilawa. Daga kowace kabila, ka aiki ɗaya daga cikin shugabanninta.”
3
Saboda haka bisa ga umarnin Ubangiji, Musa ya aike su daga Hamadan Faran. Dukansu kuwa shugabanni ne na Isra’ilawa.
4
Shugabannin kuwa su ne, Shammuwa ɗan Zakkur, daga kabilar Ruben;
5
Shafat ɗan Hori, daga kabilar Simeyon;
6
Kaleb ɗan Yefunne, daga kabilar Yahuda;
7
Igal ɗan Yusuf, daga kabilar Issakar;
8
Hosheya ɗan Nun, daga kabilar Efraim;
9
daga kabilar Benyamin, Falti ɗan Rafu;
10
Gaddiyel ɗan Sodi, daga kabilar Zebulun;
11
Gaddi ɗan Susi, daga kabilar Manasse (wata kabilar Yusuf);
12
Ammiyel ɗan Gemalli, daga kabilar Dan;
13
Setur ɗan Mika’ilu, daga kabilar Asher;
14
Nabi ɗan Bofsi, daga kabilar Naftali;
15
Geyuwel ɗan Maki, daga kabilar Gad.
16
Waɗannan su ne sunayen mutanen da Musa ya aika su binciki ƙasar. (Sai Musa ya ba Hosheya ɗan Nun, suna Yoshuwa.)
17
Sa’ad da Musa ya aike su domin su binciki Kan’ana ya ce, “Ku haura, ku ratsa ta Negeb har zuwa ƙasar tudu.
18
Ku ga yadda ƙasar take, ku ga ko mutanen da suke zama a can ƙarfafa ne, ko raunannu, ko su kima ne, ko kuma suna da yawa.
19
Wace irin ƙasa ce suke zama a ciki, Mai kyau ce, ko mummuna? Waɗanne irin birane ne suke zama a ciki? Suna da katanga, ko babu?
20
Yaya ƙasar take? Tana da wadata, ko babu? Akwai itatuwa, ko babu? Ku yi iya ƙoƙarinku ku ɗebo daga cikin albarkar ƙasar ku kawo.” (Lokacin farkon nunan inabi ne.)
Settings