Tsallake zuwa abun ciki
Mattiyu 9:27-34

Yesu ya warkar da makafi da bebe

Mattiyu 9:27-34
27
Da Yesu ya fita daga can, sai waɗansu makafi biyu suka bi shi, suna kira, suna cewa, “Ka yi mana jinƙai, Ɗan Dawuda!”
28
Da ya shiga cikin gida, sai makafin nan suka zo wurinsa, ya kuma tambaye su, “Kun gaskata cewa ina iya yin wannan?” Suka amsa suka ce, “I, Ubangiji.”
29
Sa’an nan ya taɓa idanunsu ya ce, “Bisa ga bangaskiyarku a yi muku haka”;
30
sai idanunsu suka buɗe. Yesu ya gargaɗe su sosai ya ce, “Ku lura kada wani yă san wani abu game da wannan.”
31
Amma suka fita suka yi ta baza labari game da shi ko’ina a wannan yankin.
32
Yayinda suke fitowa, sai aka kawo wa Yesu wani mutum mai aljani, da ba ya iya magana.
33
Sa’ad da aka fitar da aljanin kuwa, sai beben ya yi magana. Taron suka yi mamaki suka ce, “Ba a taɓa ganin irin wannan abu a Isra’ila ba.”
34
Amma Farisiyawa suka ce, “Ai, da ikon sarkin aljanu yake fitar da aljanu.”
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Reading Width 45 chars

Options