Mattiyu 9:18-26
18
Yayinda yake faɗin wannan, sai wani mai mulki ya zo ya durƙusa a gabansa ya ce, “Yanzu-yanzu diyata ta rasu. Amma ka zo ka ɗibiya hannunka a kanta, za tă kuwa rayu.”
19
Yesu ya tashi ya tafi tare da shi, haka ma almajiransa.
20
A daidai wannan lokaci sai ga wata mace wadda ta yi shekaru goma sha biyu tana zub da jini ta raɓo ta bayansa ta taɓa gefen rigarsa.
21
Ta ce a ranta, “Ko da rigarsa ce kawai na taɓo, zan warke.”
22
Yesu ya juya ya gan ta. Sai ya ce, “Kada ki damu diyata, bangaskiyarki ta warkar da ke.” Nan take macen ta warke.
23
Da Yesu ya shiga gidan mai mulkin ya ga masu busan sarewa da taro mai hayaniya,
24
sai ya ce, “Ku ba da wuri. Ai, yarinyar ba tă mutu ba, tana barci ne.” Amma suka yi masa dariya.
25
Bayan an fitar da taron waje, sai ya shiga ciki ya kama yarinyar a hannu, ta kuwa tashi.
26
Labarin wannan kuwa ya bazu ko’ina a yankin.
Settings