Mattiyu 24:27-31
27
Gama kamar yadda walƙiya take wulgawa walai daga gabas zuwa yamma, haka dawowar Ɗan Mutum zai kasance.
28
Duk inda mushe yake, can ungulai za su taru.
29
“Nan da nan bayan tsabar wahalan nan “ ‘sai a duhunta rana, wata kuma ba zai ba da haskensa ba; taurari kuma za su fāffāɗi daga sararin sama, za a kuma girgiza abubuwan sararin sama.’
30
“A sa’an nan ne alamar dawowar Ɗan Mutum zai bayyana a sararin sama, dukan al’umman duniya kuwa za su yi kuka. Za su ga Ɗan Mutum yana zuwa kan gizagizan sararin sama, da iko da kuma ɗaukaka mai girma.
31
Zai kuwa aiki mala’ikunsa su busa ƙaho mai ƙara sosai, za su kuwa tattaro zaɓaɓɓunsa daga kusurwoyi huɗun nan, daga wannan bangon duniya zuwa wancan.
Settings