Skip to content
Markus 4:22-41

Markus 4:22-41

22
Duk abin da yake a ɓoye, dole za a fallasa shi. Duk abin da kuma yake a rufe, dole za a fitar da shi a fili.
23
Duk mai kunnen ji, bari yă ji.”
24
Ya ci gaba da cewa, “Ku lura da abin da kuke ji da kyau. Mudun da ka auna da shi, da shi za a auna maka, har ma a ƙara.
25
Duk wanda yake da shi, za a ƙara masa, duk wanda kuma ba shi da shi, ko abin da yake da shi ma, za a karɓe daga gare shi.”
26
Ya sāke cewa, “Mulkin Allah yana kama da haka. Wani mutum ya yafa iri a gona.
27
A kwana a tashi har irin yă tsiro, yă yi girma, bai kuwa santa yadda aka yi ba.
28
Ƙasar da kanta takan ba da ƙwaya, da farko takan fid da ƙara, sa’an nan ta fid da kai, sa’an nan kan yă fid da ƙwaya.
29
Da ƙwayan ya nuna, sai yă sa lauje yă yanka, domin lokacin girbi ya yi.”
30
Ya kuma ce, “Da me za mu kwatanta mulkin Allah, ko kuwa da wane misali za mu bayyana shi?
31
Yana kama da ƙwayar mustad, wadda ita ce ƙwaya mafi ƙanƙanta da akan shuka a gona.
32
Duk da haka, in aka shuka ƙwayar, sai tă yi girma, tă zama mafi girma a itatuwan lambu. Har itacen yă kasance da manyan rassa, inda tsuntsayen sararin sama sukan iya huta a inuwarsa.”
33
Da misalai da yawa irin waɗannan, Yesu ya yi magana da su, daidai yadda za su iya fahimta.
34
Ba abin da ya faɗa musu, da ba da misali ba. Amma lokacin da yake shi kaɗai tare da almajiransa, sai yă bayyana kome.
35
A wannan rana, da yamma, sai ya ce wa almajiransa, “Mu ƙetare zuwa wancan hayi.”
36
Da suka bar taron, sai suka tafi tare da shi yadda yake, a cikin jirgin ruwa. Akwai waɗansu jiragen ruwa kuma tare da shi.
37
Sai babban hadari mai iska ya tashi, raƙuman ruwa suna ta bugun jirgin ruwan, har jirgin ruwan ya kusa yă cika da ruwa.
38
Yesu kuwa yana can baya, yana barci a kan katifa. Sai almajiran suka tashe shi suka ce masa, “Malam, ba ka kula ba ko mu nutse?”
39
Sai ya farka ya tsawata wa iskar, ya ce wa raƙuman ruwan, “Shiru! Ku natsu!” Sai iskar ta kwanta, kome kuma ya yi tsit.
40
Sai ya ce wa almajiransa, “Don me kuke tsoro haka? Har yanzu ba ku da bangaskiya ne?”
41
Suka tsorata, suka ce wa juna, “Wane ne wannan? Har iska da raƙuman ruwa ma suna masa biyayya!”
Settings

Reading style

Typeface

Font size 19px

Reading width 75 chars

Options