Skip to content
Markus 14:16-25

Markus 14:16-25

16
Almajiran suka tafi, suka shiga cikin birnin, suka kuwa tarar da kome kamar yadda Yesu ya faɗa musu. Sai suka shirya Bikin Ƙetarewa.
17
Da yamma ta yi, sai Yesu ya zo tare da Sha Biyun.
18
Yayinda suke cin abinci a tebur, sai ya ce, “Gaskiya nake gaya muku, ɗaya daga cikinku zai bashe ni, wani wanda yake ci tare da ni.”
19
Suka cika da baƙin ciki, da ɗaya-ɗaya suka ce masa, “Tabbatacce, ba ni ba ne, ko?”
20
Ya ce, “Ɗaya daga cikin Sha Biyun ne, wanda yake ci tare da ni a kwano.
21
Ɗan Mutum zai tafi kamar yadda yake a rubuce game da shi, amma kaiton mutumin da ya bashe Ɗan Mutum! Zai fi masa, da ba a haife shi ba.”
22
Yayinda suke cin abinci, sai Yesu ya ɗauki burodi, ya yi godiya, ya kakkarya, ya ba wa almajiransa, yana cewa, “Ku karɓa, wannan jikina ne.”
23
Sai kuma ya ɗauki kwaf ruwan inabi, ya yi godiya, ya kuma miƙa musu, dukansu suka sha daga ciki.
24
Sai ya ce musu, “Wannan jinina ne na alkawari, wanda aka zubar da shi saboda mutane da yawa.
25
Gaskiya nake gaya muku, ‘Ba zan ƙara sha daga ’ya’yan inabi ba, sai ranan nan, da zan sha shi sabo a mulkin Allah.’ ”
Settings

Reading style

Typeface

Font size 19px

Reading width 75 chars

Options