Luka 23:1-12
1
Sai dukan majalisa suka tashi, suka kai shi gaban Bilatus.
2
Suka fara zarginsa suna cewa, “Mun sami wannan mutum yana rikitar da al’ummarmu. Yana hana a biya haraji ga Kaisar. Yana kuma cewa, shi Kiristi ne, sarki kuma.”
3
Sai Bilatus ya tambayi Yesu ya ce, “Kai ne sarkin Yahudawa?” Yesu ya amsa ya ce, “I, haka yake, kamar yadda ka faɗa.”
4
Sai Bilatus ya sanar wa manyan firistoci da taron ya ce, “Ni fa, ban sami wani ainihin abin zargi game wannan mutum nan ba.”
5
Amma suka nace, suna cewa, “Yana tā da hankulan mutane, ko’ina a Yahudiya da koyarwarsa. Ya fara daga Galili, ga shi har ya kai nan.”
6
Da Bilatus ya ji haka, sai ya yi tambaya, “Ko shi mutumin Galili ne?”
7
Da ya ji cewa, Yesu yana ƙarƙashin mulkin Hiridus ne, sai ya aika da shi zuwa wurin Hiridus, don a lokacin Hiridus yana Urushalima.
8
Da Hiridus ya ga Yesu, sai ya yi murna ƙwarai, don tun dā ma yana marmari ya gan shi a kan abin da ya ji game da shi. Ya yi fata ya ga Yesu, yă kuma yi waɗansu ayyukan banmamaki.
9
Ya yi masa tambayoyi masu yawa, amma Yesu bai ba shi ko amsa ba.
10
Manyan firistoci da malaman dokoki suna tsaye a wurin, suna kawo zargi masu ƙarfi a kansa.
11
Sai Hiridus da sojojinsa suka wulaƙanta shi, suka yi masa ba’a. Sa’an nan, suka sa masa babban riga, suka mai da shi wurin Bilatus.
12
A ranar, Hiridus da Bilatus suka zama abokan juna, don tun dā ma, su abokan gāba ne.
Settings