Luka 18:18-27
18
Wani mai mulki ya tambayi Yesu ya ce, “Malam managarci, me zan yi don in gāji rai madawwami?”
19
Yesu ya amsa ya ce, “Don me kake kira na managarci? Ai, ba wani nagari, sai Allah kaɗai.
20
Ka san dokokin da suka ce, ‘Kada ka yi zina, kada ka yi kisankai, kada ka yi sata, kada ka ba da shaida ta ƙarya, ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka.’ ”
21
Mutumin ya ce, “Ai, tun ina ƙarami, na kiyaye duka waɗannan.”
22
Da Yesu ya ji haka, sai ya ce masa, “Akwai abu ɗaya har yanzu da ya rage maka. Ka sayar da duk abin da kake da shi, ka ba wa matalauta, sa’an nan za ka sami dukiya a sama. Bayan haka, ka zo ka bi ni.”
23
Da jin haka, sai ya ɓata rai, domin shi mai arziki ne sosai.
24
Yesu ya kalle shi ya ce, “Yana da wuya fa, masu arziki su shiga mulkin Allah!
25
Tabbatacce, zai fi sauƙi raƙumi ya shiga ta kafar allura, da mai arziki ya shiga mulkin Allah.”
26
Waɗanda suka ji wannan suka yi tambaya suka ce, “To, wa zai iya samun ceto?”
27
Yesu ya amsa ya ce, “Abin da ba ya yiwuwa ga mutane, mai yiwuwa ne ga Allah.”
Settings