Skip to content
Mahukunta 9:7-20

Mahukunta 9:7-20

7
Sa’ad da aka gaya wa Yotam wannan, sai ya hau Dutsen Gerizim ya yi kira da ƙarfi ya ce, “Ku saurare ni, ’yan ƙasar Shekem, don Allah yă saurare ku.
8
Wata rana itatuwa suka fita don su naɗa wa kansu sarki. Suka ce wa itacen zaitun, ‘Ka zama sarkinmu.’
9
“Amma itacen zaitun ya ce, ‘In bar mai nawa, wanda da shi ake girmama alloli da mutane, don in zo in yi ta fama da itatuwa?’
10
“Biye da wannan, sai itatuwan suka ce wa itacen ɓaure, ‘Zo ka zama sarkinmu.’
11
“Amma itacen ɓauren ya ce, ‘In bar kyawawan ’ya’yana da zaƙinsu, in zo in yi ta fama da itatuwa?’
12
“Sa’an nan itatuwan suka ce wa kuringar inabi, ‘Ki zo ki zama sarkinmu.’
13
“Amma kuringar ta ce, ‘In bar ruwan inabina, wanda yake faranta zuciyar alloli da mutane, in zo in yi fama da itatuwa?’
14
“A ƙarshe sai dukan itatuwa suka ce wa itacen ƙaya, ‘Ka zo ka zama sarkinmu.’
15
“Itacen ƙaya ya ce wa itatuwan, ‘In da gaske ne kuke so ku naɗa ni sarkinku, ku zo ku sha inuwana; in ba haka ba, bari wuta ta fito daga itacen ƙaya ta cinye itacen al’ul na Lebanon!’
16
“To, da a ce kun yi abin bangirma da aniya mai kyau sa’ad da kuka naɗa Abimelek sarki, da kun nuna wa Yerub-Ba’al da iyalinsa ladabi, da kuma kun yi masa abin da ya cancanci shi,
17
a yi tunani cewa mahaifina ya yi yaƙi saboda ku, ya yi kasai da ransa don yă cece ku daga hannun Midiyawa
18
(amma ga shi yau kun tayar wa iyalin mahaifina, kuka kashe ’ya’yansa saba’in a dutse guda, kuka kuma naɗa Abimelek, ɗan baiwa, sarki a kan ’yan ƙasar Shekem domin shi ɗan’uwanku ne)
19
in har kun aikata wannan cikin bangirma da kuma aminci wajen Yerub-Ba’al da iyalinsa a yau, bari Abimelek yă zama farin cikinku, ku kuma nasa!
20
Amma in ba haka ba, bari wuta ta fito daga Abimelek ya cinye ku, ’yan ƙasar Shekem da Bet Millo, bari wuta kuma daga wurinku ’yan ƙasar Shekem da Bet Millo ta cinye Abimelek!”
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options