Mahukunta 9:45-57
45
Dukan yinin, Abimelek ya matsa yaƙi da birnin sai da ya cinye ta ya kuma kashe mutanenta. Sa’an nan ya hallaka birnin ya barbaza gishiri a kanta.
46
Da jin haka, sai ’yan ƙasa a hasumiyar Shekem suka shiga wurin mafaka a hankalin El-Berit.
47
Da Abimelek ya ji dukan mutanen hasumiyar Shekem sun taru a can,
48
sai Abimelek da dukan mutanensa suka haura zuwa Dutsen Zalmon. Sai ya ɗauki gatari ya sassare waɗansu rassa, waɗanda ya sa a kafaɗunsa. Ya umarci mutanen da suke tare da shi ya ce, “Sauri, ku yi abin da kuka ga na yi!”
49
Saboda haka mutanen suka sassare rassan itatuwa suka bi Abimelek. Suka tattara su a jikin mafakar suka kuma cinna mata wuta a kan mutanen da suke a ciki. Ta haka dukan mutanen da suke cikin hasumiyar Shekem, wajen maza da mata dubu ɗaya suka mutu.
50
Biye da wannan Abimelek ya tafi Tebez, ya kewaye ta ya kuma cinye ta da yaƙi.
51
A cikin birnin, akwai wata hasumiya mai ƙarfi, inda dukan maza da mata, dukan mutanen birnin, suka ɓuya. Suka kulle kansu, suka kuma hau rufin hasumiyar.
52
Abimelek ya je wajen hasumiya ya kuma auka mata. Amma da ya yi kusa da ƙofar hasumiyar don yă cinna mata wuta,
53
sai wata mata ta saki ɗan dutsen niƙa a kan Abimelek ta fasa ƙoƙon kansa.
54
Da sauri ya kira mai riƙon masa makami ya ce, “Zaro takobinka ka kashe ni, don kada a ce ‘Mace ce ta kashe shi.’ ” Saboda haka bawansa ya soke shi, ya mutu.
55
Sa’ad da Isra’ilawa suka ga Abimelek ya mutu, sai suka tafi gida.
56
Ta haka Allah ya sāka muguntar da Abimelek da ya yi wa mahaifinsa ta wurin kisan ’yan’uwansa saba’in.
57
Allah kuma ya sa muguntar mutanen Shekem suka koma kansu. La’anar Yotam ɗan Yerub-Ba’al kuma ta kama su.
Settings