Skip to content
Mahukunta 19:15-28

Mahukunta 19:15-28

15
A can suka dakata don su kwana, suka tafi suka zauna a dandali birnin, amma wani ya shigar da su gidansa da daren.
16
A wannan yamma sai ga wani tsoho daga ƙasar tudu ta Efraim, wanda yake zama a Gibeya (mutane wurin kuwa mutanen Benyamin ne), ya shigo daga wurin aiki a gonaki.
17
Sa’ad da ya duba ya ga matafiyin a dandalin birnin, sai tsohon ya yi tambaya ya ce, “Ina za ku? Ina kuka fito?”
18
Balawen ya ce, “Muna fito daga Betlehem a Yahuda za mu wani lungu a ƙasar tudu ta Efraim inda nake da zama. Na tafi Betlehem a Yahuda, ga shi kuwa yanzu za ni gidan Ubangiji. Ba wanda ya shigar da ni gidansa.
19
Muna da ƙara da abinci don jakunanmu, muna kuma da burodi da ruwan inabi dominmu da bayinka, ni, baiwarka da kuma saurayin nan tare da mu. Ba ma bukatar kome.”
20
Tsohon ya ce, “Na marabce ku a gidana. Bari ni ba ku duk abin da kuke bukata. Kada ku dai kwana a dandali.”
21
Saboda haka sai kai shi zuwa gidansa ya ciyar da jakunansa. Bayan sun wanke ƙafafunsu, sai aka ba su abinci da abin sha.
22
Yayinda suke jin wa kansu daɗi, sai waɗansu ’yan iska daga birnin suka kewaye gidan. Suna bubbuga ƙofar, suna kira tsohon da yake da gidan suna cewa, “Ka fito mana da mutumin nan a gidanka domin mu yi jima’i da shi.”
23
Maigidan ya fita waje ya ce musu, “A’a, abokaina, kada ku yi abin kunyan nan. Da yake mutumin nan baƙona ne, kada ku yi rashin kunyan nan.
24
Duba, ga ’yata da ba tă taɓa sanin namiji ba da kuma ƙwarƙwaransa. Zan fito muku da su a waje yanzu, za ku kuwa iya yin ko mene ne da kuke so da su. Amma wannan mutum, kada ku yi abin kunya.”
25
Amma mutanen ba su saurare shi ba. Saboda haka mutumin ya ba da ƙwarƙwaransa, suka yi mata fyaɗe suka yi lalata da ita dukan dare, gari yana wayewa sai suka bar ta.
26
Da safe matar ta koma gidan da maigidanta yake, ta fāɗi a ƙofa ta kwanta a can har rana ta yi.
27
Sa’ad da maigidanta ya tashi da safe ya buɗe ƙofar gidan don yă fita ya ci gaba da tafiyarsa, sai ga ƙwarƙwararsa, ta fāɗi a bakin ƙofar gidan da hannuwanta a madogarar ƙofar.
28
Ya ce mata, “Tashi; mu tafi.” Amma ba amsa. Sai ya sa ta a kan jakinsa ya kama hanyar gida.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options