Skip to content
Mahukunta 10:6-16

Mahukunta 10:6-16

6
Isra’ilawa suka sāke yin mugayen ayyuka a gaban Ubangiji. Suka shiga bautar Ba’al da Ashtarot, da kuma allolin Aram, allolin Sidon, allolin Mowab, Ammonawa da kuma allolin Filistiyawa. Kuma domin Isra’ilawa sun bar Ubangiji ba su ƙara bauta masa ba,
7
sai ya fusata da su. Ya sayar da su ga hannun Filistiyawa da Ammonawa,
8
waɗanda suka fatattake su a shekarar suka kuma ragargaza su. Shekara goma sha takwas suka yi ta danne dukan Isra’ilawan da suke gabashin Urdun a Gileyad, ƙasar Amoriyawa.
9
Ammonawa su ma suka haye Urdun domin su yi yaƙi da Yahuda, Benyamin da kuma gidan Efraim; Isra’ila kuwa suka kasance cikin wahala ƙwarai da gaske.
10
Sa’an nan Isra’ilawa suka yi kuka ga Ubangiji, suka ce, “Mun yi maka zunubi, mun bar Allahnmu muka shiga bautar Ba’al.”
11
Ubangiji ya ce, “Sa’ad da Masarawa, Amoriyawa, Ammonawa, Filistiyawa,
12
Sidoniyawa, Amalekawa da kuma mutanen Mawon suka wulaƙanta ku kuka kuwa yi mini kuka, ban cece ku daga hannunsu ba?
13
Amma kuka bar ni kuka bauta wa waɗansu alloli, saboda haka ni ma ba zan ƙara cece ku ba.
14
Ku tafi ku yi wa allolin da kuka zaɓa. Bari su cece ku sa’ad da kuke cikin wahala!”
15
Amma Isra’ilawa suka ce wa Ubangiji, “Mu dai mun yi zunubi. Ka yi da mu abin da ka ga dama, amma muna roƙonka ka cece mu a yanzu.”
16
Sa’an nan suka zubar da allolin nan daga cikinsu suka bauta wa Ubangiji. Ubangiji kuwa bai ƙara daure da azabar da Isra’ila suke sha ba.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options