Skip to content
Yoshuwa 2:16-24

Yoshuwa 2:16-24

16
Ta ce musu, “Ku tafi cikin tuddan ƙasar don kada mutanen sarki su same ku. Ku ɓuya a can na kwana uku, har sai masu nemanku su komo, sa’an nan ku kama hanyarku.”
17
Mutanen suka ce mata, “Rantsuwar da kika sa muka yi, ba za tă yi amfani ba
18
sai in kin ɗaura jan ƙyalle a tagar da kika zura mu, kuma sai in kin kawo mahaifinki da mahaifiyarki, da ’yan’uwanki, da dukan iyalinki cikin gidanki.
19
In wani ya fita kan hanya, alhakin jininsa yă kasance a kansa; ba ruwanmu. Amma in aka taɓa wani da yake cikin gidanki tare da ke, alhakin jininsa yana kanmu.
20
In kika tone mana asiri, za mu karya alkawarin da kika sa muka yi.”
21
Ta ce, “Na yarda! Bari yă zama yadda kuka ce.” Sai ta sallame su suka tafi. Ta kuwa ɗaura jan ƙyalle a tagar.
22
Sai suka tafi, suka shiga cikin tuddai, suka yi zamansu a can kwana uku har masu nemansu suka koma, gama masu nemansu suka yi ta nema ko’ina a hanyar, amma ba su sami kowa ba.
23
Sa’an nan mutanen nan biyu, ’yan leƙen asiri suka sauka daga tuddai suka haye kogi zuwa wurin Yoshuwa ɗan Nun, suka gaya masa duk abin da ya faru da su.
24
Suka ce wa Yoshuwa, “Ba shakka Ubangiji ya ba mu ƙasan nan duka, tana hannunmu, mutane can duk sun narke da tsoro saboda mu.”
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options