Skip to content
Yoshuwa 2:8-16

Yoshuwa 2:8-16

8
Kafin ’yan leƙen asirin su kwanta, sai ta tafi wurinsu a bisa rufin ɗakin
9
ta ce musu, “Na sani Ubangiji ya riga ya ba ku ƙasan nan, tsoronku kuma ya kama mu har zukatan mazaunan ƙasar duka sun narke saboda ku.
10
Mun ji yadda Ubangiji ya busar da ruwan Jan Teku domin ku lokacin da kuka fito daga ƙasar Masar, da kuma abin da kuka yi wa Sihon da Og, sarakunan nan biyu na Amoriyawa gabas da Urdun, waɗanda kuka hallaka su sarai.
11
Da muka ji labarin, duk sai zuciyar kowa ta narke, kowa ya karaya saboda ku, gama Ubangiji Allahnku shi ne Allah na sama da ƙasa.
12
Yanzu ina roƙonku ku rantse mini da Ubangiji cewa za ku yi wa iyalina alheri kamar yadda na yi muku alheri. Ku ba ni ƙwaƙƙwarar shaida cewa
13
za ku ceci rayukan mahaifina da mahaifiyata, da ’yan’uwana maza da mata, da duk waɗanda suke nasu, za ku cece mu daga mutuwa.”
14
Mutanen suka tabbatar mata suka ce, “Ranmu a bakin ranki! In ba ki faɗa wa kowa abin da ya kawo mu ba, za mu yi miki alheri da aminci lokacin da Ubangiji ya ba mu ƙasar.”
15
Sai ta zura igiya ta taga suka bi, domin gidan da take yana haɗe da katangar birnin.
16
Ta ce musu, “Ku tafi cikin tuddan ƙasar don kada mutanen sarki su same ku. Ku ɓuya a can na kwana uku, har sai masu nemanku su komo, sa’an nan ku kama hanyarku.”
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options