Skip to content
Yoshuwa 10:13-37

Yoshuwa 10:13-37

13
Sai rana ta tsaya cik, wata kuma ya tsaya, har sai da al’ummar ta ɗauki fansa a kan abokan gābanta, kamar yadda aka rubuta a cikin littafin Yashar. Rana ta tsaya a sararin sama, ba tă fāɗi ba har kusan yini guda.
14
Ba a taɓa ganin abu haka ba ko dā can, ranar da Ubangiji ya saurari mutum. Ba shakka Ubangiji yana yaƙi domin Isra’ilawa.
15
Sai Yoshuwa ya koma sansanin Gilgal tare da dukan Isra’ilawa.
16
Sarakunan guda biyar suka gudu, suka ɓuya a cikin kogo a Makkeda.
17
Lokacin da aka gaya wa Yoshuwa cewa an sami sarakunan nan biyar a ɓoye a cikin kogo a Makkeda.
18
Sai ya ce, “Ku mirgina manyan duwatsu ku rufe bakin kogon, sai ku sa waɗannan mutane su yi tsaron kogon.
19
Amma kada ku tsaya a can! Ku fafari abokan gābanku, ku kai musu hari ta baya, kada ku bari su kai biranensu, gama Ubangiji Allahnku ya ba da su a hannunku.”
20
Saboda haka Yoshuwa da Isra’ilawa suka hallaka su da yawa ƙwarai, amma ’yan kaɗan ɗin da suka rage suka tsere zuwa cikin biranensu masu kāriya.
21
Dukan rundunar kuma suka dawo sansanin Makkeda tare da Yoshuwa, ba abin da ya same su. Ba wanda ya sāke tsokanar Isra’ilawa.
22
Yoshuwa ya ce, “Ku buɗe bakin kogon ku kawo mini sarakunan nan guda biyar.”
23
Sai suka kawo sarakunan biyar daga cikin kogo; sarakunan Urushalima, Hebron, Yarmut, Lakish da Eglon.
24
Sa’ad da aka kawo sarakunan nan wurin Yoshuwa, ya kira dukan Isra’ilawa ya ce wa shugabannin rundunoni waɗanda suke tare da shi, “Ku zo nan ku taka wuyan sarakunan nan.” Sai suka zo suka taka wuyansu.
25
Yoshuwa ya ce musu, “Kada ku ji tsoro, ko kuwa ku razana, amma ku ƙarfafa, ku yi ƙarfin hali. Haka Ubangiji zai yi da duk abokan gāban da za ku yi yaƙi da su.”
26
Sai Yoshuwa ya karkashe waɗannan sarakuna guda biyar, ya kuma rataye kowannensu a bisa itace inda jikunansu suka kasance har yamma.
27
Da yamma Yoshuwa ya ba da umarni a sauko da su daga itatuwan a jefa su cikin kogon da suka ɓuya. Aka sa manyan duwatsu aka rufe bakin kogon, suna a can har wa yau.
28
A ranan nan Yoshuwa ya ci Makkeda da yaƙi. Ya karkashe mutanen tare da sarkinta. Bai bar wani da rai ba. Ya yi wa sarkin Makkeda yadda ya yi wa sarkin Yeriko.
29
Sai Yoshuwa da dukan Isra’ilawa suka tashi daga Makkeda zuwa Libna, suka kai mata hari.
30
Ubangiji kuma ya ba da ƙasar da sarkinta a hannun Yoshuwa. Yoshuwa ya karkashe kowa ya hallaka birnin, bai bar wani da rai ba. Ya kuma yi wa sarkin yadda ya yi wa sarkin Yeriko.
31
Sai Yoshuwa da dukan Isra’ilawa suka tashi daga Libna zuwa Lakish; suka yi shiri suka kai mata hari.
32
Ubangiji ya ba da Lakish a hannun Isra’ilawa, a rana ta biyu kuwa Yoshuwa ya ci nasara a kansu. Ya karkashe duk mutanen birnin ya kuma hallaka birnin, kamar yadda ya yi a Libna.
33
Horam sarkin Gezer kuwa ya zo don yă taimaki Lakish, amma Yoshuwa ya haɗa duk da shi da rundunarsa ya ci su da yaƙi, har bai bar waninsu da rai ba.
34
Yoshuwa kuwa da dukan Isra’ilawa suka tashi daga Lakish zuwa Eglon; suka yi shiri suka kai mata hari.
35
A ranan nan suka ci ƙasar da yaƙi, suka buge ta, suka karkashe kowa da takobi kamar dai yadda suka yi a Lakish.
36
Sai Yoshuwa da dukan Isra’ilawa suka tashi daga Eglon zuwa Hebron suka kai hari a can.
37
Suka ci birnin da yaƙi, suka karkashe mazaunanta, da sarkin, har da ƙauyukan, ba wanda ya tsira kamar yadda ya yi wa Eglon. Ya hallakar da ita sarai duk da kowane mutum da yake cikinta.

Rubutun Littafi Mai Tsarki: Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™, © 2009, 2020 Biblica, Inc. · CC BY-SA 4.0“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc., used with permission.

Settings

Reading style

Typeface

Font size 19px

Reading width 75 chars

Options