Yohanna 7:40-53
40
Da jin kalmominsa, waɗansu mutane suka ce, “Ba shakka, mutumin nan shi ne Annabin.”
41
Waɗansu suka ce, “Shi ne Kiristi.” Waɗansu har wa yau suka ce, “Yaya Kiristi zai fito daga Galili?
42
Nassi bai ce Kiristi zai fito daga zuriyar Dawuda, daga kuma Betlehem garin da Dawuda ya zauna ba?”
43
Sai mutanen suka rabu saboda Yesu.
44
Waɗansu suka so su kama shi, sai dai ba wanda ya taɓa shi.
45
A ƙarshe masu gadin haikali suka koma wurin manyan firistocin da Farisiyawa, waɗanda suka tambaye su cewa, “Don me ba ku kawo shi nan ba?”
46
Sai masu gadin suka ce, “Kai, babu wanda ya taɓa magana kamar wannan mutum.”
47
Sai Farisiyawa suka amsa cikin fushi suka ce, “Af, kuna nufi har da ku ma ya ruɗe ku ke nan?
48
Akwai wani daga cikin masu mulki ko cikin Farisiyawan da ya gaskata da shi?
49
A’a! Sai dai wannan taron da ba su san kome game da Doka ba, la’anannu ne.”
50
Nikodimus, wanda ya je wurin Yesu dā, wanda kuma yake ɗayansu ya ce,
51
“Ashe, dokarmu takan hukunta mutum ba tare da an fara ji daga bakinsa game da abin da yake yi ba?”
52
Sai suka amsa suka ce, “Kai ma daga Galili ne? Bincika ka gani, za ka iske cewa ba annabin da zai fito daga Galili.”
53
Sai kowannensu ya koma gidansa.
Settings