Yohanna 17:6-19
6
“Na bayyana ka ga waɗanda ka ba ni a duniya. Su naka ne; kai ka ba ni su sun kuma yi biyayya da maganarka.
7
Yanzu sun san cewa duk abin da ka ba ni daga gare ka ya fito.
8
Na ba su kalmomin da ka ba ni sun kuwa karɓa. Sun san tabbatacce daga wurinka na fito. Sun kuma gaskata kai ka aiko ni.
9
Ina addu’a dominsu. Ba domin duniya nake addu’a ba, amma domin waɗanda ka ba ni, gama su naka ne.
10
Duk abin da nake da shi naka ne, kuma duk abin da kake da shi nawa ne. Na kuwa sami ɗaukaka ta wurinsu.
11
Ba sauran zamana a duniya, amma waɗannan a duniya suke, ni kuwa ina zuwa wurinka. Ya Uba Mai Tsarki, ka kiyaye su ta wurin ikon sunanka, sunan da ka ba ni, don su zama ɗaya kamar yadda muke ɗaya.
12
Yayinda nake tare da su, na kāre su na kuma kiyaye su ta wurin sunan nan da ka ba ni. Ba ko ɗayan da ya ɓace, sai dai wannan da aka ƙaddara zuwa ga hallaka don Nassi yă cika.
13
“Yanzu ina zuwa wurinka, sai dai na faɗi waɗannan abubuwa ne tun ina a duniya domin farin ciki yă zama cikakke a cikinsu.
14
Na gaya musu maganarka duniya kuwa ta ƙi su, don su ba na duniya ba ne yadda ni ma ba na duniya ba ne.
15
Ba addu’ata ba ce ka ɗauke su daga duniya ba, sai dai ka kāre su daga mugun nan.
16
Su ba na duniya ba ne, kamar yadda ni ma ba na duniya ba ne.
17
Ka tsarkake su ta wurin gaskiya; maganarka ce gaskiya.
18
Kamar yadda ka aiko ni cikin duniya, haka ni ma na aike su cikin duniya.
19
Saboda su ne na tsarkake kaina, domin su ma a tsarkake su da gaske.
Settings