Yohanna 1:1-9
1
Tun farar farawa akwai Kalma, Kalman kuwa yana nan tare da Allah, Kalman kuwa Allah ne.
2
Yana nan tare da Allah tun farar farawa.
3
Ta wurin Kalman ne aka halicci dukan abubuwa. In ba tare da shi ba, babu abin da aka yi wanda aka yi.
4
A cikinsa rai ya kasance, wannan rai kuwa shi ne hasken mutane.
5
Hasken yana haskakawa cikin duhu, amma duhun bai rinjaye shi ba.
6
Akwai wani mutumin da aka aiko daga Allah; mai suna Yohanna.
7
Ya zo a matsayin mai shaida domin yă ba da shaida game da wannan haske, don ta wurinsa dukan mutane su ba da gaskiya.
8
Shi kansa ba shi ne hasken ba; sai dai ya zo a matsayin shaida ne kaɗai ga hasken.
9
Haske na gaskiya da yake ba da haske ga kowane mutum mai shigowa duniya.
Settings