Tsallake zuwa abun ciki
Yowel 2:12-17

Kira zuwa Tuba ta Gaskiya

Yowel 2:12-17
12
“Ko yanzu”, in ji Ubangiji, “Ku juyo gare ni da dukan zuciyarku, da azumi da kuka da makoki.”
13
Ku kyakkece zuciyarku ba rigunanku ba. Ku juyo ga Ubangiji Allahnku, gama shi mai alheri ne mai tausayi kuma mai jinkirin fushi da yawan ƙauna, yakan kuma janye daga aika da bala’i.
14
Wa ya sani? Ko zai juya yă kuma ji tausayi yă sa mana albarka ta wurin hadaya ta gari da hadaya ta sha wa Ubangiji Allahnku.
15
A busa ƙaho a Sihiyona, a yi shelar azumi mai tsarki, a kira tsarkakan taro.
16
A tattara mutane; ku tsarkake taron; ku kawo dattawa wuri ɗaya; ku kuma tara yara, da waɗanda suke shan mama. Bari ango yă bar ɗakinsa amarya kuma lolokinta.
17
Bari firistocin da suke yin hidima a gaban Ubangiji, su yi kuka tsakanin filin haikali da bagade. Bari su ce, “Ka cece mutanenka, ya Ubangiji. Kada ka bar gādonka yă zama abin dariya, da abin ba’a a cikin al’ummai. Me zai sa a ce a cikin mutane, ‘Ina Allahnsu yake?’ ”
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Reading Width 45 chars

Options