Ayuba 24:1-12
1
“Domin me Maɗaukaki ba zai sa ranar shari’a ba? Don me waɗanda suka san shi suke faman samun irin ranakun nan?
2
Mugaye suna satar fili ta wurin matsar da duwatsun da aka yi iyaka da su; suna satar dabbobi su kuma yi kiwon su.
3
Suna ƙwace wa marayu jakunansu suna kuma ƙwace wa gwauruwa sa don suna binta bashi.
4
Suna ture matalauta daga hanya suna kuma sa dole matalautan ƙasar su ɓoye.
5
Kamar jakunan jeji a hamada, matalauta suna aikin neman abinci gonaki marasa amfani suna tanada abinci wa ’ya’yansu.
6
Suna girbi a gonakin da ba nasu ba, suna yin kala a gonar inabi ta mugaye.
7
Don ba su da tufafi, sukan kwana tsirara; ba su da wani abin da zai rufe su cikin sanyi.
8
Sun jiƙe sharkaf da ruwan da yake kwararowa daga duwatsu, sun rungume duwatsu don rashin wurin fakewa.
9
Ana ƙwace jinjiri mai shan mama; ana ƙwace ɗan yaron matalauci don biyan bashi.
10
Don ba su da tufafi suna yawo tsirara; suna dakon dammunan hatsi amma duk da haka suna cikin shan yunwa.
11
Suna matse zaitun a cikin kunyoyi suna kuma matse ruwan inabi daga ’ya’yan inabi, duk da haka suna fama da ƙishi.
12
Ana jin nishin masu mutuwa daga birni, kuma rayukan waɗanda aka ji musu rauni suna kuka suna kira don taimako. Amma bai ba wani laifi ba.
Settings