Irmiya 49:25-28
25
Me ya sa ba a tafi aka bar sanannen birnin nan ba, birnin da nake jin daɗi?
26
Tabbatacce, samarinta za su fāɗi a tituna; dukan sojojinta za su yi shiru a wannan rana,” in ji Ubangiji Maɗaukaki.
27
“Zan cinna wa katangar Damaskus wuta; za tă ci kagaran Ben-Hadad.”
28
Game da Kedar da mulkokin Hazor, waɗanda Nebukadnezzar sarkin Babilon ya fāɗa wa. Ga abin da Ubangiji yana cewa, “Tashi, ku fāɗa wa Kedar ku kuma hallaka mutanen Gabas.
Rubutun Littafi Mai Tsarki: Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™, © 2009, 2020 Biblica, Inc. · CC BY-SA 4.0“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc., used with permission.