Irmiya 49:28-33
28
Game da Kedar da mulkokin Hazor, waɗanda Nebukadnezzar sarkin Babilon ya fāɗa wa. Ga abin da Ubangiji yana cewa, “Tashi, ku fāɗa wa Kedar ku kuma hallaka mutanen Gabas.
29
Za a ƙwace tentunansu da garkunansu; za a tafi da mafakanta tare da dukan kayayyakinsu da raƙumansu. Mutane za su yi musu ihu, ‘Razana ko’ina!’
30
“Ku yi maza ku gudu! Ku zauna a kogo masu zurfi, ku da kuke zama a Hazor,” in ji Ubangiji. “Nebukadnezzar sarkin Babilon ya shirya muku maƙarƙashiya; ya ƙulla maƙarƙashiya a kanku.
31
“Ku tashi ku kuma fāɗa wa al’umma da sauƙi wadda take zama da ƙarfin hali,” in ji Ubangiji, “al’ummar da ba ta da ƙofofi ko ƙyamare; mutanenta suna zama su kaɗai.
32
Za a washe raƙumansu, garkunansu mai girma za su zama ganima. Zan watsar da waɗanda suke a wurare masu nesa a ko’ina zan kuma kawo musu masifa a kowane gefe,” in ji Ubangiji.
33
“Hazor za tă zama mazaunin diloli, kufai har abada. Ba wanda zai zauna a can; ba wanda zai zauna a cikinta.”
Settings