Skip to content
Irmiya 48:1-20

Irmiya 48:1-20

1
Game da Mowab. Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa, “Kaito ga Nebo, gama za tă lalace. Kiriyatayim za su kunyata a kuma kame ta; katagar za tă sha kunya ta kuma wargaje.
2
Ba za a ƙara yabi Mowab ba; a Heshbon mutane za su shirya mata maƙarƙashiya. ‘Zo, mu tafi mu kawo ƙarshe ga wannan al’umma.’ Ke kuma, ya Madmen za ki yi shiru; takobi zai fafare ki.
3
Saurari kuka daga Horonayim, kukan risɓewa mai girma da hallaka.
4
Za a karye Mowab; ƙanananta za su yi kuka.
5
Sun haura hanyar zuwa Luhit, suna kuka mai zafi yayinda suke tafiya; a hanyar da ta gangara zuwa Horonayim suna kuka a kan hallakar da aka ji.
6
Ku gudu! Ku gudu don tserar da ranku; ku zama kamar kurmi a hamada.
7
Da yake kun dogara ga ayyukanku da arzikinku, ku ma za a kwashe ku bayi, Kemosh zai tafi bauta, tare da firistocinsa da fadawansa.
8
Mai hallakarwa zai aukar wa kowane gari, kuma ba wani garin da zai kuɓuta. Kwari zai lalace tudu kuma ya hallaka, domin Ubangiji ya faɗa.
9
Ku sa gishiri a kan Mowab, gama za tă zama kango; garuruwanta za su zama kufai, ba mazauna a cikinsu.
10
“La’ananne ne shi wanda yake sake a yin aikin Ubangiji! La’ananne ne wanda ya janye takobinsa daga zub da jini!
11
“Mowab ta kasance cikin kwanciyar rai tun ƙuruciyarta, kamar ruwan inabin da aka bari lis, ba a juya daga tulu zuwa wani tulu ba ba tă tafi bauta ba. Saboda haka tana da ɗanɗanonta, kuma ƙanshinta bai canja ba.
12
Kwanaki suna zuwa,” in ji Ubangiji, “sa’ad da zan aika da mutanen da za su tuntsurar da tuluna, su kuma zubar da ita waje. Za su bar tulunan ba kome a ciki su kuma farfashe tulunanta.
13
Sa’an nan Mowab za tă ji kunyar Kemosh, yadda gidan Isra’ila ya ji kunya sa’ad da suka dogara ga Betel.
14
“Yaya za ku ce, ‘Mu jarumawa ne, mutane masu ƙarfi a yaƙi?’
15
Mowab za tă hallaka a kuma kai wa garuruwanta hari; samarinta kyawawa za su gangara cikin mayanka,” in ji Sarki, wanda sunansa Ubangiji Maɗaukaki ne.
16
“Fāɗuwar Mowab ta yi kusa; bala’inta zai auku nan da nan.
17
Yi kuka saboda ita, dukanku mazaunan kewayenta, duk waɗanda suka san shahararta; ku ce, ‘Dubi yadda sandan sarauta mai iko ya karye, dubi yadda sanda mai daraja ya karye!’
18
“Sauko daga darajarku ku zauna a busasshiyar ƙasa, Ya mazaunan Diyar Dibon, gama shi mai hallaka Mowab zai haura a kanku zai kuma lalace biranenku masu kagarai.
19
Ku tsaya a bakin hanya ku duba, ku da kuke zama a Arower. Ku tambayi mutumin da yake gudu da macen da take tserewa, tambaye su, ‘Me ya faru?’
20
An kunyata Mowab, gama ta wargaje. Ku yi kuka ku kuma tā da murya! Ku yi shela kusa da Arnon cewa an hallaka Mowab.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options