Skip to content
Hosiya 10:1-7

Hosiya 10:1-7

1
Isra’ila kuringa ce mai yaɗuwa; ya fitar da ’ya’ya wa kansa. Yayinda ’ya’yan suka ƙaru, ya gina ƙarin bagadai; da ƙasarsa ta wadata, ya yi wa keɓaɓɓun duwatsu ado.
2
Zuciyarsu masu ruɗu ne, yanzu kuwa dole su ɗauki laifinsu. Ubangiji zai rushe bagadansu yă kuma hallaka keɓaɓɓun duwatsunsu.
3
Sa’an nan za su ce, “Ba mu da sarki domin ba mu girmama Ubangiji ba. Amma ko da ma muna da sarki, me zai yi mana?”
4
Sun yi alkawura masu yawa, suka yi rantsuwar ƙarya da kuma yarjejjeniyoyi; saboda haka ƙararraki suka taso kamar ciyayi masu dafi da aka nome a gona.
5
Mutanen da suke zama a Samariya suna tsoro saboda gunki maraƙin Bet-Awen. Mutanensa za su yi makokinsa, haka ma firistocinsa matsafa, waɗanda suka yi farin ciki a kan darajarsa, don an ɗauke ta daga gare su aka kai ta zaman bauta.
6
Za a ɗauke shi a kai Assuriya kamar gandu wa babban sarki. Efraim zai sha kunya; Isra’ila zai sha kunya saboda gumakan itacensa.
7
Samariya da sarkinta za su ɓace kamar kumfa a bisa ruwaye.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options