Hosiya 9:10-17
10
“Sa’ad da na sami Isra’ila, ya zama kamar samun inabi a hamada; sa’ad da na ga kakanninku, ya zama kamar ganin ’ya’yan itace na farko a itacen ɓaure. Amma sa’ad da suka zo Ba’al-Feyor, suka keɓe kansu wa gumaka bankunya sai suka zama abubuwan banƙyama kamar abubuwan da suke ƙauna.
11
Darajar Efraim za tă yi firiya tă tafi kamar tsuntsu, ba haihuwa, ba juna biyu, ba ɗaukar ciki.
12
Ko da sun yi renon ’ya’ya, zan sa su yi baƙin cikin kowannensu. Kaitonsu sa’ad da na juya musu baya!
13
Na ga Efraim, kamar birnin Taya, da aka kafa a wuri mai daɗi. Amma Efraim zai fitar da ’ya’yansu ga masu yanka.”
14
Ka ba su, ya Ubangiji Me za ka ba su? Ka ba su mahaifar da za su yi ɓarin ciki da busassun nono.
15
“Saboda dukan muguntarsu a Gilgal, na ƙi su a can. Saboda ayyukansu na zunubi, zan kore su daga gidana. Ba zan ƙara ƙaunace su ba; dukan shugabanninsu ’yan tawaye ne.
16
An ka da Efraim, saiwarsu ta bushe, ba sa ba da amfani. Ko da sun haifi ’ya’ya zan kashe waɗanda suka fi ƙauna.”
17
Allahna zai ƙi su saboda ba su yi masa biyayya ba; za su zama masu yawo a cikin al’ummai.
Settings