Skip to content
Hosiya 10:1-8

Hosiya 10:1-8

1
Isra’ila kuringa ce mai yaɗuwa; ya fitar da ’ya’ya wa kansa. Yayinda ’ya’yan suka ƙaru, ya gina ƙarin bagadai; da ƙasarsa ta wadata, ya yi wa keɓaɓɓun duwatsu ado.
2
Zuciyarsu masu ruɗu ne, yanzu kuwa dole su ɗauki laifinsu. Ubangiji zai rushe bagadansu yă kuma hallaka keɓaɓɓun duwatsunsu.
3
Sa’an nan za su ce, “Ba mu da sarki domin ba mu girmama Ubangiji ba. Amma ko da ma muna da sarki, me zai yi mana?”
4
Sun yi alkawura masu yawa, suka yi rantsuwar ƙarya da kuma yarjejjeniyoyi; saboda haka ƙararraki suka taso kamar ciyayi masu dafi da aka nome a gona.
5
Mutanen da suke zama a Samariya suna tsoro saboda gunki maraƙin Bet-Awen. Mutanensa za su yi makokinsa, haka ma firistocinsa matsafa, waɗanda suka yi farin ciki a kan darajarsa, don an ɗauke ta daga gare su aka kai ta zaman bauta.
6
Za a ɗauke shi a kai Assuriya kamar gandu wa babban sarki. Efraim zai sha kunya; Isra’ila zai sha kunya saboda gumakan itacensa.
7
Samariya da sarkinta za su ɓace kamar kumfa a bisa ruwaye.
8
Za a hallaka masujadai kan tudu na mugunta zunubin Isra’ila ne. Ƙayayuwa da sarƙaƙƙiya za su yi girma su rufe bagadansu. Sa’an nan za su ce wa duwatsu, “Ku rufe mu!” Ga tuddai kuma, “Ku fāɗo a kanmu!”
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options