Farawa 36:20-30
20
Waɗannan su ne ’ya’yan Seyir Bahore maza, waɗanda suke zaune a yankin, Lotan, Shobal, Zibeyon, Ana,
21
Dishon, Ezer da Dishan. Waɗannan su ne manyan Horiyawa, ’ya’yan Seyir, maza, a ƙasar Edom.
22
’Ya’yan Lotan maza su ne, Hori da Homam. Timna ’yar’uwar Lotan ce.
23
’Ya’yan Shobal maza su ne, Alwan, Manahat, Ebal, Shefo da Onam.
24
’Ya’yan Zibeyon maza su ne, Aiya da Ana. Wannan shi ne Ana wanda ya sami maɓulɓulan ruwan zafi a hamada yayinda yake kiwon jakuna na mahaifinsa Zibeyon.
25
’Ya’yan Ana su ne, Dishon da Oholibama ’yar Ana.
26
’Ya’yan Dishon maza su ne, Hemdan, Eshban, Itran da Keran.
27
’Ya’yan Ezer maza su ne, Bilhan, Za’aban da Akan.
28
’Ya’yan Dishan maza su ne, Uz da Aran.
29
Waɗannan su ne manyan Horiyawa, Lotan, Shobal, Zibeyon, Ana,
30
Dishon, Ezer da Dishan. Waɗannan su ne manyan Horiyawa, bisa ga ɓangarorinsu, a ƙasar Seyir.
Settings