Farawa 27:1-29
1
Sa’ad da Ishaku ya tsufa idanunsa suka raunana har ba ya iya gani, sai ya kira Isuwa babban ɗansa ya ce masa, “Ɗana.” Isuwa kuwa ya amsa, ya ce “Ga ni.”
2
Ishaku ya ce, “Yanzu na tsufa kuma ban san ranar mutuwata ba.
3
Saboda haka yanzu, ka ɗauki makamanka, kwari da bakanka, ka tafi jeji ka farauto mini nama.
4
Ka shirya mini irin abinci mai daɗin da nake so, ka kawo mini in ci, domin in sa maka albarka kafin in mutu.”
5
Ashe, Rebeka tana ji sa’ad da Ishaku ya yi wa ɗansa Isuwa magana. Da Isuwa ya tafi jeji don yă farauto nama yă kawo,
6
sai Rebeka ta ce wa ɗanta Yaƙub, “Ka ji nan, na ji mahaifinka ya ce wa ɗan’uwanka Isuwa,
7
‘Kawo mini nama ka shirya mini abinci mai daɗi don in ci, in sa maka albarka a gaban Ubangiji kafin in mutu.’
8
Saboda haka ɗana, ka saurara da kyau ka kuma yi abin da na faɗa maka.
9
Je garke ka kawo mini awaki biyu kyawawa, domin in shirya abinci mai daɗi wa mahaifinka, kamar yadda dai yake so.
10
Sa’an nan ka kai wa mahaifinka yă ci, domin yă sa maka albarka kafin yă mutu.”
11
Yaƙub ya ce wa mahaifiyarsa Rebeka, “Amma ɗan’uwana Isuwa mutum ne mai gashi a jiki, ni kuma jikina sumul yake.
12
A ce baba ya tattaɓa ni fa? Zai zama kamar ina ruɗunsa ne, wannan fa zai jawo mini la’ana a maimakon albarka.”
13
Mahaifiyarsa ta ce masa, “Ɗana, bari la’anar tă fāɗo a kaina. Kai dai yi abin da na faɗa, jeka ka kawo mini su.”
14
Sai ya tafi ya kamo su, ya kawo wa mahaifiyarsa, ta kuwa shirya abinci mai daɗi, yadda mahaifinsa yake so.
15
Sa’an nan Rebeka ta ɗauki riguna mafi kyau na Isuwa babban ɗanta, waɗanda take da su a gida ta sa wa ƙaramin ɗanta Yaƙub.
16
Sai ta mamanne gashin awakin nan biyu a hannuwansa da bayan wuyarsa wanda ba gashi.
17
Sa’an nan ta ba wa ɗanta Yaƙub abinci mai daɗi da kuma burodin da ta yi.
18
Shi kuwa ya tafi wurin mahaifinsa ya ce, “Babana.” Shi kuma ya amsa “I, ɗana, wane ne?”
19
Yaƙub ya ce wa mahaifinsa, “Ni ne Isuwa ɗan farinka. Na yi yadda ka faɗa mini. Ina roƙonka tashi ka zauna ka ci naman, domin ka sa mini albarkarka.”
20
Ishaku ya tambayi ɗansa, “Yaya aka yi ka samo shi da sauri haka, ɗana?” Yaƙub ya amsa ya ce, “Ubangiji Allahnka ne ya ba ni nasara.”
21
Sai Ishaku ya ce wa Yaƙub, “Zo kusa don in taɓa ka, ɗana, domin in sani ko tabbatacce kai ne ɗana Isuwa ko babu.”
22
Yaƙub kuwa ya matsa kusa da mahaifinsa Ishaku, wanda ya tattaɓa shi, sa’an nan ya ce, “Muryan nan dai, muryar Yaƙub ce, amma hannuwan, hannuwan Isuwa ne.”
23
Bai gane shi ba, gama hannuwansa suna da gashi kamar na ɗan’uwansa Isuwa, saboda haka ya albarkace shi.
24
Ya tambaya, “Tabbatacce kai ne ɗana Isuwa?” Ya amsa ya ce “Ni ne.”
25
Sa’an nan ya ce, “Ɗana, kawo mini naman da ka farauto in ci, domin in sa maka albarka.” Yaƙub ya kawo masa ya kuwa ci; ya kuma kawo masa ruwan inabi ya kuma sha.
26
Sa’an nan mahaifinsa Ishaku ya ce masa, “Zo nan, ɗana ka sumbace ni.”
27
Saboda haka ya je gunsa ya sumbace shi. Sa’ad da Ishaku ya ji ƙanshin rigunansa, sai ya sa masa albarka ya ce, “Aha, ƙanshin ɗana yana kama da ƙanshin jejin da Ubangiji ya sa wa albarka ne.
28
Allah yă ba ka daga raɓar sama da kuma yalwar ƙasa, yalwar hatsi da sabon ruwan inabi.
29
Bari al’ummai su bauta maka mutane kuma su rusuna maka. Ka zama shugaba a kan ’yan’uwanka bari kuma ’ya’yan mahaifiyarka su rusuna maka. Bari waɗanda suka la’anta ka, su la’antu; waɗanda kuma suka sa maka albarka, su sami albarka.”
Settings