Skip to content
Farawa 26:23-33

Farawa 26:23-33

23
Daga can ya haura zuwa Beyersheba.
24
A wannan dare Ubangiji ya bayyana gare shi ya ce, “Ni ne Allah na mahaifinka Ibrahim. Kada ka ji tsoro, gama ina tare da kai, zan albarkace ka, zan kuma ƙara yawan zuriyarka saboda bawana Ibrahim.”
25
Sai Ishaku ya gina bagade a can, ya kuma kira bisa sunan Ubangiji. A can ya kafa tentinsa, a can kuma bayinsa suka haƙa wata rijiya.
26
Ana cikin haka, sai Abimelek ya zo wurinsa daga Gerar, tare da Ahuzzat mai ba shi shawara da Fikol shugaban mayaƙansa.
27
Ishaku ya tambaye su, “Me ya kawo ku gare ni, da yake kun yi gāba da ni, kuka kuma kore ni?”
28
Suka amsa, “Mun ga a zahiri cewa Ubangiji yana tare da kai; saboda haka muka ce, ‘Dole rantsuwa ta kasance tsakaninmu da kai.’ Bari mu yi yarjejjeniya da kai
29
cewa ba za ka cuce mu ba, kamar yadda ba mu fitine ka ba, amma muka yi maka kirki, muka kuma sallame ka cikin salama. Yanzu kuwa kai albarkatacce ne na Ubangiji.”
30
Sai Ishaku ya shirya musu liyafa, suka ci suka kuma sha.
31
Kashegari da sassafe sai mutanen suka yi wa juna rantsuwa. Sa’an nan Ishaku ya sallame su, suka kuwa tafi cikin salama.
32
A wannan rana bayin Ishaku suka zo suka faɗa masa game da rijiyar da suka haƙa. Suka ce, “Mun sami ruwa!”
33
Sai ya kira ta Shiba, don haka har wa yau ana kira garin Beyersheba.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options