Farawa 26:24-27
24
A wannan dare Ubangiji ya bayyana gare shi ya ce, “Ni ne Allah na mahaifinka Ibrahim. Kada ka ji tsoro, gama ina tare da kai, zan albarkace ka, zan kuma ƙara yawan zuriyarka saboda bawana Ibrahim.”
25
Sai Ishaku ya gina bagade a can, ya kuma kira bisa sunan Ubangiji. A can ya kafa tentinsa, a can kuma bayinsa suka haƙa wata rijiya.
26
Ana cikin haka, sai Abimelek ya zo wurinsa daga Gerar, tare da Ahuzzat mai ba shi shawara da Fikol shugaban mayaƙansa.
27
Ishaku ya tambaye su, “Me ya kawo ku gare ni, da yake kun yi gāba da ni, kuka kuma kore ni?”
Settings