Skip to content
Ezekiyel 47:13-23

Ezekiyel 47:13-23

13
Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, “Waɗannan su ne iyakokin da za ku raba ƙasar gādo cikin kabilan Isra’ila goma sha biyu, da rabo biyu don Yusuf.
14
Za ku raba ta daidai a cikinsu. Gama na ɗaga hannu na rantse zan ba da ita ga kakanninku, wannan ƙasa za tă zama gādonku.
15
“Wannan ce za tă zama iyakar ƙasa. “A wajen arewa za tă fara daga Bahar Rum ta hanyar Hetlon ta wuce Lebo Hamat zuwa Zedad,
16
Berota da Sibrayim (wadda take a iyaka tsakanin Damaskus da Hamat), har zuwa Hazer-Hattikon, wadda take a iyakar Hauran.
17
Iyakar za tă miƙe daga teku zuwa Hazar-Enon, ta iyakar Damaskus, da iyakar Hamat a arewa. Wannan ita ce iyakar a wajen arewa.
18
A wajen gabas iyakar za tă kama tsakanin Hauran da Damaskus, ta bi ta Urdun tsakanin Gileyad da ƙasar Isra’ila, zuwa tekun gabas har zuwa Tamar. Wannan ita ce iyakar a wajen gabas.
19
A wajen kudu za tă fara daga Tamar har zuwa ruwan Meriba Kadesh, sa’an nan ta bi Rafin Masar zuwa Bahar Rum. Wannan ita ce iyakar a wajen kudu.
20
A wajen yamma, Bahar Rum ne zai zama iyakar zuwa wani wuri ɗaura da Lebo Hamat. Wannan ita ce iyakar a wajen yamma.
21
“Za ku rarraba wannan ƙasa a tsakaninku bisa ga kabilan Isra’ila.
22
Za ku raba ta kamar gādo wa kanku da kuma wa baƙin da suka zauna a cikinku waɗanda suke da ’ya’ya. Za ku ɗauka su kamar ’yan ƙasa haifaffun Isra’ilawa; za su yi gādo tare da ku a cikin kabilan Isra’ila.
23
A duk kabilar da baƙon yake zama, a can za ku ba shi gādonsa,” in ji Ubangiji Mai Iko Duka.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options