Skip to content
Ezekiyel 16:44-52

Ezekiyel 16:44-52

44
“ ‘Duk mai yin amfani da karin magana zai faɗi wannan karin magana a kanki cewa, “Kamar yadda mahaifiya take haka ’yar take.”
45
Ke ’yar mahaifiyarki ce da gaske, wadda ta ƙi mijinta da ’ya’yanta; ke kuma ’yar’uwar ’yar’uwanki mata ce da gaske, waɗanda suka ƙi mazansu da ’ya’yansu. Mahaifiyarki mutuniyar Hitti ce, mahaifinki kuma mutumin Amoriyawa ne.
46
Babbar ’yar’uwarki mutuniyar Samariya ce, wadda take zaune da ’ya’yanta mata wajen arewa da ke; ƙanuwarki ita ce Sodom wadda take zaune kudu da ke tare da ’ya’yanta mata.
47
Ba ki bi hanyoyinsu da abubuwansu na banƙyama kaɗai ba, sai ka ce wannan ya yi miki kaɗan, amma kin lalace fiye da su.
48
Muddin in raye, in ji Ubangiji Mai Iko Duka, ’yar’uwarki Sodom da ’ya’yanta mata ba su yi abin da ’ya’yanki mata suka yi ba.
49
“ ‘To, fa, ga zunubin ’yar’uwarki Sodom. Ita da ’ya’yanta mata sun yi girman kai, sun ƙoshi fiye da kima kuma ba su kula da wani abu ba; ba su taimaki matalauta da kuma masu bukata ba.
50
Su masu girman kai ne kuma suka aikata abubuwa masu banƙyama a gabana. Saboda haka na kau da su kamar yadda ka gani.
51
Samariya ba tă aikata ko rabin zunubanki ba. Kin aikata abubuwa masu banƙyama fiye da su, suka kuma sa ’yan’uwanki mata suka zama kamar masu adalci ta wurin dukan waɗannan abubuwa da kika aikata.
52
Ki sha kunyarki, gama kin yi rangwame wa ’yan’uwanki mata. Saboda zunubanki sun yi muni fiye da nasu, sai suka zama kamar sun fi ki adalci. Saboda haka, ki sha kunya ki kuma sha ƙasƙancinki, gama kin sa ’yan’uwanki mata suka zama kamar su masu adalci ne.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options