Fitowa 16:29-35
29
Ku lura fa, ai, Ubangiji ne ya ba ku Asabbaci; shi ya sa a kan ba ku burodi na kwana biyu, a rana ta shida. Kowa ya kamata yă kasance inda yake a rana ta bakwai; kada kowa yă fita.”
30
Sai mutanen suka huta a rana ta bakwai.
31
Mutanen Isra’ila suka kira burodin Manna. Manna yana nan fari kamar farin riɗi, ɗanɗanonsa kuma yana kama da masa da aka yi da zuma.
32
Musa ya ce, “Wannan shi ne abin da Ubangiji ya umarta, ‘Ku auna mudu guda na Manna, a adana ta dukan zamananku, domin kowane zamani yă ga irin abincin da na ba ku ku ci a hamada, yayinda na fitar da ku daga Masar.’ ”
33
Saboda haka Musa ya ce wa Haruna, “Ka ɗauki tulu, ka sa mudu guda na Manna a ciki. Sa’an nan ka sa shi a gaban Ubangiji, don a adana don tsararraki masu zuwa.”
34
Sai Haruna ya ajiye Mannar a gaban Akwatin Alkawari, don a adana ta kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa.
35
Isra’ilawa suka yi shekaru arba’in suna cin Manna, har sai da suka shiga cikin ƙasar da take da mutane, suka ci Manna har zuwa kan iyakar ƙasar Kan’ana.
Settings